‘Yan majalisar wakilai guda biyu sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, a ci gaba da yawaitar ficewar ‘yan siyasa daga jam’iyyun hamayya.
Peter Akpanke daga jihar Cross River, wanda ya bar jam’iyyar PDP, da kuma Paul Nnamchi daga Enugu, wanda ya fice daga Labour Party, sun bayyana sauyin nasu cikin wasiku da shugaban majalisa Abbas Tajudeen ya karanta a zaman ranar Talata.
Akpanke ya ce rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyarsa ne ya sa ya fice, yayin da Nnamchi ya danganta sauyinsa da rashin daidaito a shugabancin jam’iyyar LP.
Wannan na zuwa ne a jerin sauya sheƙa da dama da aka samu a cikin majalisar tun daga Oktoba 2023, wanda ya haifar da ƙarfafa APC da kuma raunana tasirin PDP da LP a majalisar wakilai.