Gwamnatin tarayya ta ce rukunin farko na ‘yan Najeriya da aka kwaso daga kasar Sudan mai fama da rikici za su iso Abuja a yau.
Shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ce ta bayyana hakan ga manema labarai jiya a Abuja.
Ta ce sama da ‘yan Najeriya miliyan uku ne ke zaune a kasar Sudan kuma ana kokarin kwashe mutane da dama idan har yakin ya ci gaba, ta kara da cewa za a bayar da fifiko ga yara da dalibai da mata.
Da take magana jiya a wani shirin gidan Talabijin na Channels, Dabiri-Erewa, ta ce jami’o’in Najeriya sun yi tayin karbar daliban Najeriya da suka dawo daga Sudan.
Direbobi kashin farko na bas biyar da ke jigilar daliban Najeriya da suka bar birnin Khartoum a ranar Laraba sun yi watsi da su a cikin jeji na tsawon sa’o’i sabo da rashin biyansu kudi. Sai dai hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta ce an shawo kan dukkan matsalolin.