Yan Sanda A Jigawa Sun Kama Matashi Kan Zargin Kashe Mahaifiyarsa.

0 518

An Kama Matashi Mai Shekaru 30 Bisa Zargin Kashe Mahaifiyarsa a Karamar Hukumar Gumel

An kama wanda ake zargi, an tsare shi kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kansa.

Acewar sanarwar da Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Jigawa ta fitar tace cikin bakin ciki da alhini muke sanar da wani mummunan lamari da ya faru na kashe uwa da ɗanta ya aikata a unguwar Dantanoma, Karamar Hukumar Gumel ta jihar.

A ranar Lahadi, 29 Ga Yuni, 2025, da misalin karfe 8 na dare, jami’an ‘yan sanda na Hedkwatar Gumel sun samu rahoto kai tsaye game da wani tashin hankali tsakanin uwa da ɗanta.

Da isar jami’an ‘yan sanda wajen, an gano cewa wani matashi mai suna Hussaini Abubakar, ɗan shekara 30 daga unguwar Dantanoma, ya kai hari kan mahaifiyarsa Dahara Mu’azu mai shekaru 75, inda ya dinga dukankanta da tubalin kasa har sai da ya kashe ta.

Leave a Reply