‘Yan sanda a jihar Jigawa sun cafke masu babura 16 saboda taka dokar hana fita da gwamnatin jihar ta kakaba

0 110

‘Yan sanda a jihar Jigawa sun cafke masu babura 16 saboda taka dokar hana fita da gwamnatin jihar ta kakaba.

Kakakin ‘yan sanda, ASP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da kamen ga manema labarai a Dutse.

Ya ce an kama masu baburan ne a Dutse saboda laifin rashin biyayya ga umarnin da gwamnatin jihar ta bayar.

Ya ce an gurfanar da masu laifin a gaban kotu sannan aka yanke musu hukuncin daurin watanni uku tare da zabin biyan tara.

Sawaba ta bayar da rahoton cewa Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayar da umarnin takaita zirga-zirgar babura daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe a fadin jiharnan.

Manufar dokar ta takaita zirga-zirga ita ce magance ayyukan masu laifi a jiharnan.

Rundunar yansandan tayi nuni da cewa dokar har yanzu tana nan tana aiki, inda ta shawarci sauran jama’a da su kiyaye ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: