Yan sanda a Somalia sun tabbatar da kisan fararen hula takwas a wani harin kunar bakin wake da aka kai Mogadishu babban birnin kasar.

Wasu mutum 17 na daban sun jikkata, ciki har da yara 13 na wata makaranta da ke kusa da wurin da aka kai harin.

Harin da al-Shabab suka kai a wata mota, sun yi nufin kai shi ne kan wani jerin gwanon motocin jami’an tsaron wani kamfani da yake kare Majalisar Dinkin Duniya.

‘Yan sanda sun ce babu wani wakilin MDD da harin ya shafa.

Rahotanni sun ce an kai harin ne da safe lokacin da ake saurin tafiya wuraren aiki.

Tuni al-Shabab ta dauki nauyin kai harin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: