‘Yan sanda sun cafke wata dalibar jami’ar Ekiti (EKSU) bisa zargin yin Garkuwa da kanta

0 175

‘Yan sandan Ekiti sun kama wata dalibar jami’a, Helen Kayode bisa zargin yin garkuwa da kanta don kawai ta debe wa saurayinta kewa Dalibar ta aika wa ‘yar uwarta saƙon ƙarya cewa an yi garkuwa da ita, amma bincike ya nuna ta kwana tare da saurayinta a Ado-Ekiti Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya yi Allah wadai da abin da dalibar ta aikata, inda ya ce za a gurfanar da ita gaban kotu da an gama bincike

Dalibar tana ajin ƙarshe ne a jami’ar jihar Ekiti (EKSU), Helen Kayode, An ce, abin da ya bai wa mutane mamaki ta yadda ta shirya garkuwa da kanta don kawai ta debe wa saurayinta kewa.

Leave a Reply