Yan sanda sun kama wani mutum da ya cinnawa dakin ‘ya’yan matarsa wuta

0 76

Rundunar ‘yan sanda a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta kama wani mutum bisa zargin kunnawa ‘ya’yan matarsa wuta.

Jami’in hulda da jama’a a rundunar ‘yan sandan jihar SP Funmilayo Odunlami ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran kasar faruwar lamarin a Akure babban birnin jihar.

Ya ce lamarin ya faru ne ranar Asabar, inda ya ce jami’an ‘yan sanda suna gudanar da bincike, yayin da yaran ke samun kulawar likitoci a babban asibitin Owo.

Ya kara da cewa an mayar da batun zuwa ga sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar, domin gudanar da bincike yadda ya kamata.

Wani shaida ya fada wa kamfanin dillacin labaran kasar NAN cewa mutumin ya kunna wuta a dakin da yaran ke kwance ne sakamakon samun ‘yar rashin jituwa da matar tasa.

Majiyar ta kara da cewa daya daga cikin yaran ya rasa ransa, sakamakon wutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: