‘Yan sandan jihar Jigawa sun fatattaki wasu gungun’ yan fashi da makami da ke addabar garin Ringim

0 106

‘Yan sanda a jihar Jigawa sun fatattaki wasu gungun’ yan fashi da makami da ke addabar garin Ringim da kewaye.

Akwai zaman lafiya a Ringim shekaru da dama, amma a ‘yan kwanakinan, wasu gungun masu aikata laifuka suka fara tayar da zaune tsaye a garin.

Lamarin ya sanya hukumomin tsaro da majalisar karamar hukumar sun tashi haikan domin magancewa.

A kwanakin baya ne majalisar dokokin karamar hukumar ta hana zirga-zirgar babura bayan karfe sha biyun dare, don magance ayyukan masu aikata laifuka a yankin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ASP Lawan Shiisu Adam ya ce rundunar ta samu nasarar cafke wasu mutane biyu na gungun ‘yan ta’adda.

Ya bayyana cewa a yayin da ake yi musu tambayoyi, wanda ake zargin ya furta cewa shi da sauran abokan aikinsa sun addabi garin na Ringim da kewaye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: