‘Yan Sandan Nigeria Sun Tabbatar Da Shirinsu Na Gudanar Da Sahihin Zaben Cike Gibi Dake Gudana A Kasar

0 96

A jiya ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta raba wasu muhimman kayyayaki a jihohin Adamawa, Kebbi da sauran inda ake gudanar da zaben yau.

Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da jami’an zaben da rundunar ‘yan sanda suka tabbatar da shirinsu na gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar da cewa za ta sake gudanar da zabe a jihohin Adamawa, Kebbi, Sokoto da sauran jihohin da za a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a ranar 18 ga watan Maris, da kuma wuraren da ba a kammala zabe ba na wasu kujerun ‘yan majalisar kasar.

Ya ce an sake saita na’urorin tantance masu kada kuri’a na (BVAS) domin gudanar da zabe kuma ba za fuskanci matsalar tantancewa ba.

A wani labarin kuma, zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su zabi rayinsu cikin tsari da lumana, a lokacin da kuma bayan kammala zaben na yau. A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja, Tinubu ya kuma roki INEC da ta gudanar da zaben gaskiya da adalci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: