Yankuna 551 a sassan ƙananan hukumomi 12 ne hare-haren ƴan bindiga suka shafa – Uba Sani

0 141

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce yankuna 551 a sassan ƙananan hukumomi 12 ne hare-haren ƴan bindiga suka shafa lamarin da ya ɗai-ɗaita mutane dubu dari 289 da 375.

Babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Dakta Usman Hayatu Mazadu, ne ya bayyana haka lokacin rarraba kayan taallafi a Maraban Kajuru.

Ya ce a yankin Chikun, yankuna 134 lamarin ya shafa sannan mutum dubu 26 da 345 ne suka rasa gidajensu.

Dakta Mazadu ya jaddada buƙatar a samar wa mutanen da lamarin ya shafa tallafi inda ya bayyana mummunan tasirin da hare-haren suka yi wa yankunan.

Jihar Kaduna dai na cikin jihohin da suke fama da matsalar ƴan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa, inda ko a baya-bayan nan an sace gomman ɗalibai tare da malaminsu a yankin Kuriga. Sai dai jami’an tsaro sun kuɓutar da su bayan kwanaki a hannun ƴan bindigar da suka yi awon gaba da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: