’Yanmajalisar tarayya a Najeriya sun bayyana cewa ’yan ƙungiyar Boko Haram mai iƙirarin jihadi na amfani da jiragen yaƙi marasa matuka wajen kai hare-hare, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.
Wani danmajalisa daga kudu maso gabashin Borno – inda hare-haren Boko Haram suka fi ƙamari – ya ce ‘yanbindigar sun fi sojojin Najeriya makamai”.
“Ina cikin waɗanda suka gani da idonsu. Ba labari aka ba ni ba. Wannan zai shiga tarihi. Boko Haram na amfani da jiragen yaki marasa matuka, wadanda sojojin Najeriya ba su amfani da su.
“Ma’ana, suna da kayan aiki fiye da rundunar sojin Najeriya,” in ji Ahmed Jaha, dan majalisar wakilai daga mazabar Chibok.
Zainab Gimba, wakiliyar mazaɓar Bama, ita ma ta tabbatar da cewa mayaƙan na amfani da jiragen yaki marasa matuka, tana mai zargin akwai hannun ƙasashen waje.
“Kwamandan ya shaida min cewa daga cikin ’yanta’addan akwai fararen fata da dama; akwai sa hannun wasu daga kasashen waje,” in ji ta.
An samu ƙarin hare-hare da ake ɗora wa Boko Haram da Iswap alhakin kai su kan jami’an tsaro a jihohin Borno da Yobe a ’yan kwanakin nan.