Yansandan Jihar Kano sun tabbatar da mutuwar fitaccen jagoran ƙungiyar ƴan daba Abba Burakita

0 119

Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani fitaccen jagoran ƙungiyar ƴan daba, Abba Bala Burakita, bayan wata arangama da wasu ƙungiyoyin daba abokan gabarsu a unguwar Dorayi da ke Kano.

Burakita, wanda ya yi ƙaurin suna wajen tayar da hankalin jama’a a yankin, ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a yayin fafatawar, duk da an kama shi kuma aka kai shi Asibitin Murtala don jinya.

Ayyukansa na laifi sun sa ya zama abin farauta ga jami’an tsaro da dama, kuma mazauna yankin sau da dama suna kukan rashin tsaro, suna kira ga hukuma da ta ɗauki mataki a kansa.

A martanin da gwamnatin Jihar Kano ta ɗauka kan rikice-rikicen da Burakita da sauran ‘yan daba ke haddasawa, ta amince da gina sabon ofishin ƴansanda a Dorayi domin ƙarfafa tsaro da inganta hanzarin amsa kiran gaggawa.

Kakakin rundunar ‘yansandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da ƙudirin rundunar na ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankunan da rikicin ‘yan daba ke addaba a Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: