Rundunar ‘yansandan jihar Neja ta tabbatar da kisan mutanenta uku da wasu ‘yan kato da gora 2 a wani kwantan bauna da ‘yan bindiga suka yi musu a Kwanar Dutse dake yankin karamar hukumar Mariga ta jihar.

Kwamishinan ‘yansanda na jihar, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da haka a jiya yayin zantawa ta wayar tarho tare da kamfanin dillancin labarai na kasa a Minna, babban birnin jihar.

Bala Kuryasa yace lamarin ya auku a ranar Litinin da misalin karfe 4 na yamma lokacin da tawagar hadin gwiwa ta tsaro, da ta kunshi ‘yansanda da ‘yan kato da gora, suke rangadi a yankin.

Yace an kuma kashe ‘yan bindigar dayawa yayin musayar wutar wanda ya kwashe awanni.

Yayi nuni da cewa tawagar hadin gwiwar ta tsaro a ranar Lahadi da safe ta dakile wani hari daga wasu gungun ‘yan bindiga bayan kimanin awanni 2 na musayar wuta a kauyen Bari dake kan titin Tegina zuwa Kontagora.

A cewarsa, an aika da wata tawagar ‘yansanda da sojoji zuwa yankin kuma sun kaddamar da aiki da nufin damke bata garin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: