‘Yan’uwan juna 4 sun mutu bayan nutsewa cikin ruwa bayan jirgin ruwansu ya kife a Yaurin jihar Kebbi

0 145

‘Yan’uwan juna 4 a jiya sun mutu bayan nutsewa cikin ruwa inda har yanzu ake neman gawar wani bayan jirgin ruwan da suke ciki tare da mahaifinsu da karin wasu fasinjoji biyu domin tsallaka kogi zuwa gonarsu, ya kife a Yaurin jihar Kebbi.

An bayar da rahoton cewa har yanzu ana cigaba da neman gawar dan’wansu da ba a gani ba, bayan an ceto sauran fasinjojin biyu da ransu.

Da yake zantawa da sashen Hausa na BBC, mahaifin yaran, Musa Labaran, yace jirgin ruwan na dauke da shi da ‘ya’yansa zuwa gonarsu dake tsallaken kogi lokacin da hadarin ya auku bayan guguwa mai karfi ta kada.

Musa Labaran yace yayi iya bakin kokarinsa wajen ganin ya ceci daya cikin ‘ya’yan lokacin da jirgin ruwan ya fara kifewa.

Musa Labaran yace duk da kasancewar mutane sun yi gaggawar fara aikin ceto, an dauki lokaci mai tsawo kafin a samu gawarwakin yaran guda 5.

A bara, mutane 100 ne suka mutu a haduran jiragen ruwa a jihar Kebbi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: