yar manuniya ce kan mummunan yanayin da kasarnan ke ciki karkashin mulkin APC a cewar jam’iyyar PDP

0 85

Jam’iyyar PDP tace rikice-rikicen da suka biyo bayan zaben jam’iyyar APC a wasu jihoshi, yar manuniya ce kan mummunan yanayin da kasarnan ke ciki karkashin mulkin APC.

Hakan yazo ne cikin wata sanarwa da aka fitar jiya ta hannun kakakin PDP, Kola Ologbondiyan.

A sakamakon da yayi kamanceceniya da na zabukanta a mazabu da kananan hukumomi da aka gudanar a watannin Yuli da Satumba, jam’iyya mai mulki ta sake samun gudanar da zabuka daban-daban a wasu daga cikin jihoshin da take da karfi a ranar Asabar, lamarin dake kara bayyana kokonta a hadin kan jam’iyyar.

An samu rikici ko sabunta gabar siyasa tsakanin shugabannin jam’iyyar da magoya baya a akalla jihoshi 10, yayin da aka yi zaben sulhu a wasu jihoshin dayawa.

Jihoshin Osun, Ogun, Kwara, da Neja sune kan gaba a jihoshin da aka gudanar da zabuka a gurare biyu a karshen mako. Kazalika an gudanar da zabe a gurare biyu a Kano, Enugu, Akwa Ibom da jihar Imo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: