Yara 6 sun mutu yayin da mazaunan karamar hukumar Jibia ke gudun hijira sakamakon janyewar jami’an soji a jihar Katsina

0 44

Mutane shida ne akasari yara kanana suka mutu yayin da mazauna kauyen Shimfida da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina ke gudun hijira sakamakon abin da suka kira janyewar jami’an soji daga yankin ba tare da gargadi ba.

Janye sojojin ya haifar da kaura mai yawa daga mazauna kauyen saboda fargabar hare-haren ‘yan bindiga.

Mazauna kauyen sun shaida wa manema labarai a jiya cewa, wasu motocin sojoji ne suka shiga yankin tare da kwashe dukkan jami’an sojin daga inda suke zaune na wani dan lokaci.

Kauyen Shimfida yana gefen dajin Dumburum inda aka ce nan ne sansanin dayawa daga cikin ‘yan fashin da ke aiki a jihohin Zamfara da Katsina.

Wani mazaunin kauyen ya ce ya zama wajibi su yi hijira domin ‘yan bindigar sun fusata da mutanen Shimfida saboda kasancewar jami’an soji a kauyen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: