Gumel Da Ringim Sun Ƙudiri Aniyar Magance Ambaliyar Ruwa

0 180

Gwamnatin jihar Jigawa ta jaddada kudirinta na cigaba da kare rayuka da kuma dukiyoyin alummar jiharta.

Daraktan tsaftar mahalli na Hukumar Kare Mahalli ta jiha Alhaji Nuhu Yusif shine ya bada wannan tabbaci a lokacin da yake duba aikin tsaftar mahalli da hukumar take gudanarwa a garin Gumel.

Yace sakamakon mamakon ruwan sama da ake tafkawa a sassan jihar nan ya zama wajibi hukumar ta gudanar da aikin yashe magudanan ruwa da kwalbatoci domin gudun ambaliyar ruwa da wasu yankuna suke fuskan ta.

Alhaji Nuhu Yusif ya kara da cewar za su gudanar da aikin yashe kwalbatoci da magudanan ruwan ne na kwanaki 12 a shiyyoyin Gumel da Ringim.

Daga nan sai ya bukaci al’umma da su guji zuba shara a magudanan ruwa domin gudun ambaliyar ruwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: