Za a samar da wadataccen ruwan sha mai amfani da hasken rana sama da 100 a yankin Rigim da Kazaure

0 91

Shugaban Hukumar Samarda Ruwansha a Yankunan Karkara STOWA ta Jihar Jigawa tare da wakilan hukumar sun fara rangadin duba aiyukan samar da ruwan sha karkashin hukumar a shiyoyinta na Ringim da Kazaure.

Da yake karbar yan tawagar a Ringim Manajan shiyyar Alhaji Sani Taura yace an samarda sabbin tashoshin ruwan sha masu amfani da hasken rana 50 da canza masu aiki da inji zuwa aiki da hasken rana 30 a shiyyar yayinda ake kan gyaran guda 35.

A shiyyar Kazaure manajan shiyyar Mallam Nasiru Abdu ya shedawa shugaban da wakilan cewar shiyyar na da tashoshin ruwa masu aiki da hasken rana 40 yayinda aka canza guda 25 masu aiki da inji zuwa hasken rana.

Da yake maida jawabi shugaban hukumar, Alhaji Abdulaziz Ismaila Dawaki ya nuna jin dadi game da yadda manajojin da ma’aikatansu ke rike aiyukansu na ganin jama-a na samun isasshen ruwan sha karkashin hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: