Cibiyar Yan Kasuwa, Masana-antu da Ma’adinai da Aikin Gona ta jihar Jigawa ta samu amincewar Gwamnatin jihar Jigawa domin gudanar da kasuwar baje koli ta Azumin watan Ramadan a garin Hadejia.

Shugaban Cibiyar, Alhaji Mutari Muhammad Birniwa ya sanar da hakan ga wakilinmu, inda yace za a gudanar da kasuwar baje kolin ne ta makonni uku daga ranar bakwai ga watan Afirilu na wannan shekara.

Yace kamfanoni da masana-antu da kanana da kuma manyan yan kasuwa zasu baje kolin kayayyakin masarufi da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.

Alhaji Mutari Muhammad Birniwa ya bukaci masu shaawar baje kolin dasu je cibiyar dake Dutse da kuma ofishin Himma Bata ga Rago domin sayen takardun neman izinin shiga baje koli.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: