Gwamnatin Jihar Filato ta tabbatar da kudirinta na ganin an dakile sake faruwar kisan gilla bayan kisan matafiya 12 daga Zariya da aka yi a ƙaramar hukumar Mangu.
Wadanda aka kashe na kan hanyarsu ne zuwa wajen bikin aure lokacin da aka yi musu kwanton bauna lamarin da ya jawo suka daga sassan ƙasa daban-daban.
Da take magana da BBC, kwamishiniyar yaɗa labarai ta jihar, Joyce Ramnap, ta ce Filato jiha ce mai son zaman lafiya, kuma gwamnati na da niyyar tabbatar da adalci da tsaron jama’a.
Ta tabbatar da kama mutane 22 da ake zargi da hannu a harin, tana mai cewa gwamnati na jiran kammala binciken ‘yan sanda kafin ta ɗauki mataki na gaba.