Za muci gaba da tattaunawa da ASUU kan yanayin daya jefa su yajin aiki – Gwamnatin Tarayya

0 71

Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na sake tattaunawa kan yanayin aikin dukkan ma’aikata a jami’o’in gwamnati dake fadin kasar nan.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kwamitin sulhu na gwamnatin tarayya da na jami’o’i na shekarar 2009 karkashin jagorancin shugaban kwamitin, Nimi Briggs, jiya a Abuja.

Chris Ngige ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai rike da mukamin shugabar ‘yan jaridu da hulda da jama’a a ma’aikatar, Patience Onuobia.

Ministan yana magana ne kan yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta ke gudanarwa.

Ya ce a matsayinsa na mai shiga tsakani, ya dade yana ta kokarin ganin an aiwatar da duk wani abu da ke kunshe a cikin yarjejeniyar fahimtar juna ta shekarar 2020 wacce gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU suka sanya wa hannu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: