Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyar Najeriya na ci gaba da kasancewa jigo a ƙungiyar tattalin arzikin yammacin Afirka wato ECOWAS, inda ya ce Najeriya za ta ci gaba da taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya, haɗin kai da walwala a yankin.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin bikin cika shekaru 50 da kafuwar ECOWAS da aka gudanar a birnin Legas, inda ya yabawa tsohon shugaban ƙasa Janar Yakubu Gowon mai ritaya, wanda shi ne kadai jagoran da ya rage da rai daga cikin waɗanda suka rattaba hannu a yarjejeniyar kafa ƙungiyar.
Tinubu ya jaddada irin gudummawar Najeriya tun kafuwar ECOWAS, musamman ta hanyar shirye-shirye kamar samar da rundunar tsaro, wanda ya shafe kusan shekaru arba’in yana tura ƙwararrun ma’aikata zuwa ƙasashen membobin ƙungiyar don bayar da taimako. Ya ce ƙasarsa ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ƙungiyar ta fuskoki da dama, ciki har da sauƙaƙe cinikayya da zirga-zirga a tsakanin ƙasashe, da kuma bayar da gudummawa wajen samar da zaman lafiya da dawo da tsarin dimokuraɗiyya a ƙasashen da suka samu rikice-rikice.