Kwamitin sayar da ɗanyen man fetur da tatacce na shugaban ƙasa ya ce zai fara ɗauko kashin farko na tataccen mai daga kamfanin Dangote a gobe Lahadi 15 ga watan Satumba.
Ɗaya daga cikin mambobin kwamitin wanda kuma shi ne shugaban hukumar tattara kudaɗen haraji ta ƙasar, (FIRS), Zacch Adedeji, ne ya bayyana haka a jiya Juma’a.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a babban birnin tarayya Abuja, shugaban Kwamitin ya ce daga ranar 1 ga watan Oktoba, babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL zai fara sayen ganga dubu 385,000 a kowace rana daga matatar man ta Dangote.
Ya ƙara da cewa matatar Dangoten za ta riƙa sayar wa Najeriya man fetur da na dizel da zai wadace ta, kuma za a yi cinikin ne da kuɗin ƙasar wato naira.
Ya ci gaba da cewa Matatar na iya samar da man fetur fiye da abin da ake buƙata a fadin kasar.