Za’a fara biyan daliban da suka nemi bashin kuɗin karatu nan da mako guda

0 198

Ɗaliban manyan makarantun gwamnatin tarayya da suka nemi bashin kuɗin karatu za su fara samun kuɗin nan da mako guda, a cewar asusun ba da bashin ɗaliban.

Sai dai shugaban asusun, Akintunde Sawyerr, ya ce ɗaliban makarantun da za su fara sabon zangon karatu ne kawai za su ga kuɗin a asusunsu a yanzu.

A jiya Laraba ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da asusun mai suna Nigerian Education Loan Fund (Nelfund) a hukumance a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Mista Sawyerr ya ce jimillar ɗalibai dubu 170,000 ne suka yi rajista da asusun, waɗanda suka ƙunshi ɗaliban jami’a, da na kwalejojin ilimi da fasaha.

Leave a Reply

%d bloggers like this: