Za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali

0 87

Hukumar Alhazan ta kasa NAHCON  za ta fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali.

Za a ƙaddamar da fara jigilar maniyyatan bana ne a jihar Kebbi.

Tuni shugaban hukumar Alhazan ƙasar, Jalal Ahmed Arabi tare da wasu jamai’an hukumar suka isa jihar, domin duba shirye-shiyen da hukumar ta yi gabanin fara jigilar maniyyatan.

NAHCON ta ce jirgin farko da zai tashi daga filin jirgin saman, Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, zai ɗauki maniyyata 428.

Nahcon ta kuma ce tun a ranar Lahadi ne tawagar jami’an lafiya da manema labarai da masu kula da masaukai da kwamitin ciyarwa da sauran kwamitoci suka tashi zuwa ƙasa mai tsarkin domin shirya fara shirye-shirye.

Hukumar alhazan ta ce za a ci gaba da jigilar alhazan har zuwa ranar 10 ga watan Yuni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: