Za’a kafa cibiya ta musamman domin yaƙi da ƴan bindiga a shiyar Arewa maso yamma

0 112

Ma’aikatar tsaro ta sanar da shirin kafa wata cibiya ta musamman a ƙarƙashin jagorancin kwamnanda daya, wadda babban aikinta shi ne yaƙi da ƴan bindiga a shiyar Arewa maso yamma, maimakon tsarin da ake da shi a yanzu. 

Ministan tsaro Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana haka yayin wata ziyara da ya kai a jihar Kaduna, inda ya yabawa sojojin da ke yaki da ayyukan ƴan bindiga a yankin Birnin Gwari.

Wannan mataki dai na daga cikin hanyoyin da mahukunta ke ci gaba da nemowa da za su taimaka domin wanzar da tsaro a yankin Arewa Maso Yamma. Kazalika Ministan ya bayyana yunkurin su na sasanta rikicin manoma da makiyaya dake faruwa a jihar Filato.

Leave a Reply

%d bloggers like this: