Za’a Kammala Aikin Helkwatar NEMA Ranar 21 Ga Wata Afrilu

0 90

Ministan jin kai da cigaban al’umma da kare afkuwar bala’o’I Sadiya Umar Farouq tace aikin helkwatar hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA da akeyi tun shekarar 20219 za’a kammala shi ranar 21 ga watan Afrilu.
Ministan ta bayyana haka yayin da ta ziyarci helkwatar hukumar dake Abuja.
Sadiya Umar-Farouq ta kai ziyarar ne domin duba aikin da ake yi da kuma tabatar da cewa yan kwangilar suna aikin su akan lokaci domin ana so a kaddamar da aikin kafin 29 ga watan Mayu.
Ta kuma kara da cewa taba baiwa yan kwangilar dukkan goyan bayan da suke bukata domin ganin aikin ya tabbata.
Kazalika, Daraktan Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA Mustapha Ahmed ya bayyana farin cikin sa dangane da gyaran helkwatar hukumar.
Ya ce wasu ma’aikatan na zaune a wuraran haya, wasu kuma a kwantainoni, yayinda wasu kuma basu da bancinan zama.
Daraktan na NEMA yace akwai bukatar a gyara helkwatar, ya kuma kara da cewa ma’aikatan su zasu koma 30 ga watan Afrilu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: