Za’a Samu Ruwan Sama Mai Karfi A Abuja, Kano, Kaduna, Yobe, Bauchi da Jigawa A Bana – NEMA

0 99

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa, Mustapha Ahmed, ya ce akwai yiyuwar za a iya samun ruwan saman kasa da kasa a Abuja, Kano, Kaduna, Yobe, Bauchi da Jigawa a bana.

Ya bayyana hakan ne jiya a Abuja a wajen taron baje kolin daftarin Shirye Shiryen annoba da Ya shafi Yanayi na 2023.

Ya ce ana sa ran Bayelsa, Akwa-Ibom, Delta da Cross River za su samu ruwan sama mai girman da ya kai maki 2700.

Ya ce bisa la’akari da hasashen ambaliyar ruwa na shekara ta 2023 da Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya ta fitar, kananan hukumomi 66 na fuskantar hadarin ambaliya daga watan Afrilu zuwa Yuni akananan hukumomi 148 kazalika daga awatanYuli zuwa Satumba za’a samu wasu kananan hukumomi  100, Oktoba da Nuwamba wanda annobar zata shafa.

Hasashen na bana ya yi nuni da cewa akwai babban hadarin ambaliya a gabar teku sakamakon hasashen da ake sa ran za a samu karuwar ruwan teku da kuma bututun da zai iya yin illa ga manoma, matsugunan mutane da sufuri a jihohin Bayelsa, Delta, Legas da Rivers.

Ana kuma hasashen zazzafar ambaliyar ruwa a birane da garuruwa da dama saboda rashin tsarin magudanar ruwa da rashin bin ka’idojin tsare-tsaren muhalli.

Ahmed ya ce a bana za a iya samun ambaliyar ruwa irin ta bara, idan ba ayi hankali ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: