Zababben dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Maru da Bungudu a jihar Zamfara, Abdulmalik Zubairu, a jiya ya bayar da gudunmuwar shanu 59 ga al’ummar mazabar sa domin gudanar da bukukuwan Sallah.
Da yake jawabi yayin rabon dabbobin a Bungudu, zababben dan majalisar ya bayyana cewa hakan na daga cikin shirye-shiryensa na jin dadin jama’a domin gudanar da Sallah.
Abdulmalik Zubairu wanda tsohon shugaban jam’iyyar APC reshen karamar hukumar Bungudu, Basharu Bello-Auki ya wakilta, ya ce wadanda suka ci gajiyar rabon sun hada da wakilan jam’iyyar APC na mazabu 21 na kananan hukumomin Bungudu da Maru.
Bello-Auki kuma shi ne shugaban kwamitin rabon shanun.
Ya ce sauran wadanda aka bawa sun hada da marayu, zawarawa, ‘yan gudun hijira, matasa da kungiyoyin mata.
Da yake mayar da martani a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, shugaban gidauniyar Zannah na jam’iyyar APC reshen Maru, Nasiru Sani ya yabawa zababben dan majalisar bisa wannan karamcin.
- Comments
- Facebook Comments