Zamu inganta harkar noma ta hanyar sayar da su a gona da kuma haramtawa ‘yan kasashen waje sayen kayan a gonaki – Majalisa

0 88

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da wata takarda da aka shirya don inganta harkar noma a Najeriya ta hanyar sayar da amfanin gona a gonaki da kuma haramtawa ‘yan kasashen waje da wakilansu sayen kayan amfanin gona a gonaki.

Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Otunba Adeniyi Adebayo ne ya sanar da hakan a jiya a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan taron majalisar ministocin wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa a Abuja.

Ya ce idan aka amince da hakan, masu sayayya na cikin gida ne kawai wadanda su ke da rajista, za su iya siyan kaya kai tsaye daga hannun manoma tare da siyar wa ‘yan kasashen waje.

Adebayo ya ce, ‘yan kasashen waje sun dena cutar manoma wadanda ke amfani da kudi wajen saye musu amfanin gona.

Ya yi nuni da cewa, ana gudanar da wata doka da za ta tabbatar da sanya ido sosai a kan lamarin, domin matakin da aka amince da shi ya dace da dokokin kasuwanci na kasa da kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: