‘Zan dora kan abubuwan da Gwamna Badaru yayi wajen bunkasa tattalin arzikin jihar Jigawa a ciki shekara 2’ – Umar Namadi

0 128

Kamar yadda sashen Hausa na BBC suka tattauna da shi. Sun bayyana cewa “dan takarar gwamnan Jihar Jigawa na jam’iyyar APC, Umar Namadi, ya ce babban burinsa idan ya ci zaben shi ne ya bunkasa tattalin arzikin jihar.

“Abin da ya ba ni kwarin gwiwa na shiga wannan takara shi ne yadda a shekara bakwai da suka wuce mun yi aiki da shugabana Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, na ga irin dimbin ci gaban da aka kawo wa jihar Jigawa a wannan lokaci, sannan kuma na san irin tunaninsa da kuma abin da yake so jihar Jigawa ta zama.

Saboda haka wannan ya ba ni kwarin gwiwar cewa ya kamata ni ma na bayar da tawa gudunmawar na dora kan abubuwan da wannan mutumin ya yi.”

Umar Namadi ya kara da cewa “Na farko dai muna so mu ga cewa an dora tattalin arzikin Jihar Jigawa a kan wani tafarki mai dorewa. Kamar yadda BBC Hausa suka wallafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: