Zanga-zanga ta barke a kananan hakumomin Jos da Bukuru a jihar Filato

0 354

Zanga-zanga ta barke a kananan hakumomin Jos da Bukuru a jihar Filato biyo bayan hakuncin kotun daukaka kara da soke nasarar dan majalisa mai wakiltar yankin a zauren majalisar wakilai.

Masu zanga-zangar wanda galibi matasa ne da mata sun nuna rashin amincewar su da hakuncin na kotun daukaka kara wanda ta soke nasarar yan takarar jam’iyyar PDP na sanata da dan majalisar wakilai.

Masu zanga-zangar dauke da alluna daban-daban sun yi watsi da hakuncin kotun. Da yake yiwa manema labarai karin haske a adadin masu zanga-zangar Ibrahim Yakubu ya roki ma’aikatar sharia da ta sake Nazari kan hakuncin kotun daukaka karar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: