Zanga-zangar adawa da garambawul a ɓangaren shari’a ta ɓarke a Mexico

0 89

Majalisar dattawan ƙasar Mexico ta amince da sake fasalin ɓangaren shari’a mai cike da cece-kuce inda jama’a ne za su zaɓi alƙalai ta hanyar kaɗa ƙuri’a.

Magoya bayan dokar sun ce sauye-sauyen za su sa alƙalan su zama masu kishin al’ummar Mexico amma masu sukar ta na ganin hakan zai gurgunta tsarin tabbatar da daidaito a ƙasar kuma zai faɗaɗa ƙarfin ikon jam’iyyar Morena mai mulki.

Amincewa da ƙudurin dokar dai ya janyo ruɗani a ƙasar, inda tun da farko masu zanga-zanga suka kutsa cikin ginin da ya kamata a kaɗa ƙuri’a kan ƙudirin.

Kuri’ar majalisar dattawan ita ce babban ƙalubale na ƙarshe da dokar wanda ke samun goyon bayan Shugaba Andrés Manuel López Obrador ke fuskanta.

A wani zama mai ban mamaki da aka yi cikin dare, sai da aka dakatar da muhawarar a lokacin da masu zanga-zangar suka mamaye zauren da sanatocin suka taru, wanda hakan ya tilasta musu komawa wani gini na daban.

An kaɗa ƙuri’ar ne dai da sanyin safiyar Laraba inda aka kira Sanatocin ɗaya bayan ɗaya da sunayensu domin su kaɗa ƙuri’arsu.

Sanata Miguel Ángel Yunes ya zame saniyar ware a jam’iyyar adawa ta National Action Party inda ya kaɗa ƙuri’ar amincewa da ƙudurin, wanda ke nufin an samu rinjayen kashi biyu bisa uku da ake buƙata don sauya tsarin mulkin ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: