Ƴan Taliban Sun Halarci Jana’izar Ali Khamenei A Iran

Ƴan Taliban sun halarci jana’izar Ali Khamenei a Iran

Jami’an gwamnatin Taliban da kuma shugabannin ‘yan adawar Afghanistan sun halarci jana’izar Ali Khamenei a birnin Tehran na ƙasar Iran.

Kafofin yaɗa labarai na Iran sun wallafa hotunan shugaban ƙungiyar ƴan turjiya ta National Resistance Front of Afghanistan, Ahmad Massoud, da shugaban jam’iyyar haɗin kan Musulmin Afghanistan, Mohammad Mohaqiq, yayin da suke yi wa Ali Khamenei da iyalansa ta’aziyya.

Tawagar wakilan gwamnatin Taliban ƙarƙashin jagorancin mataimakin firaminista Abdul Ghani Baradar Akhund da ministan harkokin wajen ƙasar Amir Khan Muttaqi, ita ma ta halarci masallacin da ake gudanar da jana’izar domin girmama marigayin.

A gefe guda kuma, mataimakin ministan harkokin wajen Saudiyya, Walid Al-Khuraiji, tare da tawagarsa, sun halarci wajen jana’izar a Tehran domin miƙa ta’aziyyarsu.

Comments (0)
Add Comment