Abdulaziz Umar Ganduje, babban ɗan tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya sayi fom ɗin takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar NDC.
Rahotanni sun ce Abdulaziz na neman wakiltar mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado a zaɓen shekarar 2027, lamarin da ke nuna sabon sauyi a tafiyar siyasarsa.
Matakin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi gabanin babban zaɓe mai zuwa, yayin da jam’iyyu da ’yan siyasa ke ci gaba da shirye-shiryensu domin fafatawa a matakai daban-daban.