Ɗaya daga cikin dattawa biyu da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kebbi, Malam Yahaya Billi, ya rasu yayin da yake hannunsu.
Marigayin, wanda shi ne shugaban ƙungiyar JIBWIS (Izala) reshen ƙaramar hukumar Koko-Besse, ya rasu ne bayan kwanaki da sace shi tare da wani mutum.
Ƙungiyar JIBWIS reshen Koko-Besse ce ta sanar da rasuwar tasa, inda ta bayyana an gudanar da sallar jana’izarsa ta Salatul Ga’ib da ƙarfe 4:30 na yammacin jiya Talata a ƙofar fadar Sarkin Koko.
Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin jimami, yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da suka haɗa da garkuwa da mutane a sassan jihar Kebbi.