Dan Majalisar Wakilai na Yewa North/Imeko-Afon, Gboyega Isiaka, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa sassauta dokar hana sayar da man fetur a yankunan da ke cikin tazarar kilomita 20 daga iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin.
A cewar Isiaka, dokar da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kafa shekaru shida da suka gabata ta haifar da matsin tattalin arziki a garuruwan Imeko, da Ilara, da Oja Odan da Ohunbe.
Yanzu haka, tashoshin mai guda biyar sun samu izinin komawa aiki, abin da ya kawo sauƙi ga al’ummar yankin.
Ya kuma bukaci masu tashoshin mai da mazauna yankin su kiyaye doka domin kada a sake shan matsala.z