Abin Al’ajabi Zazzau ya janye daga takarar kujerar Majalisar Tarayya

Hon. Mahmud Sadis Buba, wanda aka fi sani da Abin Al’ajabin Zazzau, ya sanar da janyewarsa daga neman takarar kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Sabon Gari ta Zaria a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar Asabar, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntuba da sulhu da shugabanni da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar domin haɗa kai a bayan ɗan takara guda.

Ya gode wa gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, da shugabannin APC bisa damar da suka ba shi na shiga takarar.

Abin Al’ajabi ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da kasancewa mai biyayya ga jam’iyyar APC tare da mara wa ɗan takarar da jam’iyyar ta zaɓa baya a zaɓe mai zuwa.

Comments (0)
Add Comment