Ƙungiyar gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya ta kammala taronta na 11 da ta gudanar a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
A ranar Alhamis ɗin nan ne gwamnonin suka gudanar da taron kan matsalolin da yankin ke fama da su da suka haɗa da na tsaro da kuma tattalin arziƙi.
Taron na zuwa a yayin da yankin ke fama da sabbin hare-haren daga mayaƙan Boko Haram da na ISWAP.
Masana da al’ummar yankin na cewa dama ce gwamnonin suka samu domin tattauna yadda za a shawo kan matsalar tsaro da ke addabar yankin.