ADC Na Zawarcin Nasiru Gawuna Domin Takarar Gwamnan Kano A 2027

Jam’iyyar ADC na ci gaba da ƙoƙarin jawo tsohon ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, domin ya tsaya takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar a zaɓen 2027.

Rahoton DAILY NIGERIAN ya ce wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar na tattaunawa da makusantan Gawuna tare da ƙoƙarin shawo kansa ya amince da tikitin gwamna na ADC. Rahotanni sun nuna cewa ana kuma duba yiwuwar samar da cikakken goyon bayan yaƙin neman zaɓensa idan ya amince.

Gawuna, wanda ya yi takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin APC a zaɓen 2023, ya fice daga jam’iyyar tare da komawa ADC a watan Maris na shekarar 2026.

Sai dai har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga Gawuna da ke tabbatar da amincewarsa da tayin takarar gwamnan da ake cewa ADC na yi masa.

Comments (0)
Add Comment