Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta nemi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya fito fili ya bayyana wa ‘yan Najeriya ainihin dalilan da suka sa aka yi canji kwatsam a shugabancin rundunonin tsaro na ƙasar.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Juma’a, jam’iyyar ta ce tana da damuwa da yadda aka sauke kusan dukkan hafsoshin da Shugaban Ƙasa ya naɗa shekaru biyu da suka gabata, ba tare da wani bayani dalla-dalla ba.
Jam’iyyar ta kara da cewa rashin bayyana gaskiya kan dalilin sauyin na iya haifar da ruɗani da rashin kwanciyar hankali a cikin rundunonin tsaro, musamman ganin cewa waɗanda aka tsige sun shafe fiye da shekara guda kacal a mukamansu.
Jam’iyyar ta nuna damuwa da yadda gwamnati ke mai da hankali kan siyasar mulki, maimakon tsaro da rayuwar ‘yan ƙasa, tana mai cewa tsige kusan duka shugabannin sojoji zai iya ƙara jawo jita-jita da ƙirƙirar labaran ƙarya kan cewa demokradiyya tana cikin barazana.
A ƙarshe, ADC ta yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta fito da bayanan gaskiya domin ta kwantar da hankulan ‘yan Najeriya, tana mai cewa “ƙasar tana buƙatar gaskiya da kwanciyar hankali fiye da komai a wannan lokaci”.