Airtel ta dakatar da bayar da bashin kati da data a Najeriya

Kamfanin sadarwa na Airtel Nigeria ya sanar da dakatar da sabis ɗin bayar da bashin kati da data na wucin gadi a faɗin ƙasar.

Kamfanin ya bayyana cewa sabis ɗin da aka dakatar yana bai wa kwastomomi masu layin prepaid damar aro kati ko data, sannan su biya daga baya lokacin da suka yi caji.

Sai dai duk da dakatarwar, kamfanin ya tabbatar da cewa kwastomomi za su ci gaba da sayen kati da data ba tare da wata tangarda ba ta hanyoyin da aka saba amfani da su.

A cewar kamfanin, wannan mataki na ɗan lokaci ba zai shafi ingancin ayyukansa a ƙasar ba.

Da yake magana kan lamarin, Daraktan harkokin tallace-tallace na kamfanin, Ismail Adeshina, ya ce matakin ya zama dole domin daidaita ayyukan kamfanin da sabbin ƙa’idoji da dokoki da ake buƙata.

Ya ce: “Wannan mataki ne mai muhimmanci kuma na ɗaukar alhaki domin tabbatar da cewa ayyukanmu sun dace da sabbin tsare-tsare. Muna ci gaba da jajircewa wajen bin doka, gaskiya da kare haƙƙin masu amfani da sabis, tare da ci gaba da kawo sabbin dabaru a fannin sadarwar zamani a Najeriya.”

Kamfanin ya ƙara da cewa zai sanar da kwastomomi duk wani sabon ci gaba game da dawo da sabis ɗin nan gaba.

Comments (0)
Add Comment