Alarammomi Sun Amince da Tsarin Haɗa Ilimin Boko da Na Addini A Jigawa

Alarammomi sun amince da tsarin haɗa ilimin boko da na addini a Jigawa

Gwamnatin Jihar Jigawa tare da haɗin gwiwar UNICEF da tallafin Tarayyar Turai sun fara shirin wayar da kan Alarammomi kan yadda za a haɗa ilimin karatu da lissafi na zamani (FLN) da tsarin karatun Tsangaya.

Manufar shirin ita ce ƙara wa Almajirai ilimin rayuwa ba tare da rage darajar karatun Alƙur’ani ba.

An gudanar da taron ne a Dutse ranar Alhamis, inda aka gayyaci Alarammomi daga ƙananan hukumomin jihar domin fahimtar manufar shirin da rawar da za su taka wajen aiwatar da shi.

Babban Sakataren Hukumar Ilimin Tsangaya ta Jihar Jigawa (JSTEB), Dakta Abubakar Maje Hamisu, ya ce shirin zai kawar da rudani da rashin fahimta da wasu malamai ke yi game da hada ilimin boko da na Tsangaya.

“Wasu na tunanin za a rushe tsarin Tsangaya ne, amma ba haka ba ne. An kawo shi ne domin ƙarfafa tsarin ilimin Tsangaya,” in ji shi.

Ya bayyana cewa Almajirai za su ci gaba da koyon Alƙur’ani da ilimin addini, sannan a ƙara musu karatu, rubutu, lissafi da koyon sana’o’i domin su samu damar rayuwa mai inganci a nan gaba.

Dakta Hamisu ya bayyana Alarammomi a matsayin ginshikin tsarin Tsangaya, yana mai cewa ba tare da goyon bayansu ba, ba za a samu nasarar shirin ba.

Ya buƙaci mahalarta taron da su isar da abin da suka koya ga sauran malamai da ba su samu damar halarta ba.

A nasa jawabin, Dakta Auwalu Halilu daga Jami’ar Bayero ta Kano ya ce tsarin hada ilimi yana nufin bai wa Almajirai damar koyon Alkur’ani da ilimin addini tare da karatu, rubutu, lissafi, dabarun rayuwa da koyon sana’a.

“Ba mu zo mu maye gurbin ilimin Alkur’ani ba. Mun zo ne domin mu karfafa shi tare da ba yara karin ilimin da zai amfani rayuwarsu,” in ji shi.

Ya kara da cewa shirin zai bude wa Almajirai kofofin samun ilimi da sana’a, tare da rage talauci, bara da ware yara daga cikin al’umma.

Taron ya tattauna hanyoyin samar da yanayin koyo mai tsaro ga Almajirai, karfafa hadin gwiwa tsakanin Hukumar Ilimin Tsangaya ta Jigawa, UNICEF da sauran masu ruwa da tsaki.

A ƙarshe, Alarammomin sun bayyana gamsuwarsu da shirin, tare da alkawarin rungumar tsarin hada ilimin addini da na boko a Tsangayunsu domin inganta ilimin Almajirai a fadin Jihar Jigawa.

Comments (0)
Add Comment