Albaliyar Ruwa ta mamaye wasu yankunan da suke Jihar Yobe

Albaliyar Ruwa ta Mamaye wasu yankunan da suke cikin Helikwatar karamar hukumar Jakusko ta Jihar Yobe, sakamakon mamakon ruwan sama.

Mamakon ruwan saman da aka samu a garin ya rushe gidaje masu tarin yawa, tare da lalata gidajen masu karamin karfe, wanda hakan ya tashe garuruwa da yawa.

Da yake zantawa da manema labarai, Sakataren Zartarwa na Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe Dr Muhammad Goje, ya ce Gwamna Mai Mala Buni ya umarci hukumar ta tantance adadin mutanen Ambaliyar ruwan ta shafa.

A wani labarin kuma, gobara ta tashi a sansanin Jami’an Tsaro dake Jakunko tare da shafar akalla Jami’a 30, wanda suke zaune a sansanin.

Hukumar Bada Agaji ta SEMA, ta yi Alkawarin tallafawa mutanen da iftila’in ya shafa domin rage musu radadi, biyo bayan matsin tattalin arziki da kasar take ciki.

Comments (0)
Add Comment