Al’ummar ƙasar Malawi Na Jefa ƙuri’a a Zaɓen Shugaban ƙasa Dana ƴanmajalisa Bayan Shekara Biyar

Al’ummar ƙasar Malawi na jefa ƙuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da na ƴanmajalisar dokoki, bayan shekara biyar da ƙasar ta yi tana fuskantar matsalar tattalin arziki.

Shugaba Lazarus Chakwera na neman wa’adi na biyu, yayin da Peter Mutharika ya zama babban abokin hamayyarsa, mutumin da ya ke da shakaru 80 da ɗoriya, wanda kuma ya taɓa riƙe muƙamin gwamnati a baya.

A birane da dama na ƙasar matsalolin ƙarancin man fetur da tsadar rayuwa ne suka kankane yaƙin neman zaben.

Matsalar man fetur ɗin dai ta janyo dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai.

Za a tafi zagaye na biyu, idan a cikinsu babu wanda ya samu kashi 50 cikin ɗari na ƙuri’un da aka kaɗa, a zaɓen na yau Talata.

Comments (0)
Add Comment