Amurka Ta ƙara Sa Ido Kan Tsaron Najeriya Bayan Majalisar Wakilai Ta Mika Rahoton Tsaro Ga Trump

Rahoton, wanda kwamitocin kula da kasafin kuɗi da harkokin waje suka gabatar, ya kunshi zarge-zargen muzgunawa Kiristoci da kuma yaɗuwar rikicin masu tsattsauran ra’ayi a sassa daban-daban na ƙasar.

Matakin ya biyo bayan sake ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ke da matuƙar damuwa kan batun ’yancin addini (Country of Particular Concern – CPC) da gwamnatin Trump ta yi, tare da umartar ɗan majalisa Riley Moore da shugaban kwamitin kasafi Tom Cole su jagoranci binciken majalisa kan batun.

Moore ya tabbatar da miƙa rahoton ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce rahoton ya samo asali ne daga shaidu na ƙwararru, zaman sauraren ra’ayi a majalisa, tarurrukan sirri da kuma ziyarce-ziyarce biyu da wakilan jam’iyyun biyu suka kai Najeriya domin tantance halin da ake ciki.

A yayin ɗaya daga cikin ziyarce-ziyarcen, tawagar Amurka ta kai ziyara sansanonin ’yan gudun hijira a jihar Benuwe, inda suka gana da waɗanda rikici ya shafa da kuma manyan jami’an gwamnatin Najeriya ciki har da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Moore ya ce ziyarar ta ba su damar fahimtar girman matsalar tsaro da ƙalubalen da al’ummomin Kiristoci ke fuskanta a wasu yankuna.

Rahoton ya ba da shawarar kulla yarjejeniyar tsaro ta bai-daya tsakanin Amurka da Najeriya domin kare al’ummomi masu rauni da kuma rusa hanyoyin sadarwar masu tsattsauran ra’ayi. Haka kuma ya ba da shawarar dakatar da wasu tallafin kuɗaɗen Amurka har sai gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakan da za a iya aunawa wajen rage tashin hankali.

Daga cikin sauran shawarwarin akwai kakaba takunkumi da hana biza ga duk wanda aka samu da hannu a muzgunawa addini, da kuma bayar da taimakon fasaha ga hukumomin Najeriya wajen magance hare-haren da ake dangantawa da makiyaya masu ɗauke da makamai.

Rahoton ya kuma buƙaci a sake duba wasu dokokin Shari’a da na batanci da ake ganin na nuna wariya, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashen duniya irin su France, Hungary da United Kingdom.

A baya, a wa’adin mulkinsa na farko, Trump ya ayyana Najeriya a matsayin CPC a shekarar 2020, amma daga bisani gwamnatin Joe Biden ta cire sunan ƙasar daga jerin a 2021 – matakin da wasu ’yan majalisa ciki har da Chris Smith suka soka.

A cikin Najeriya, batun ya jawo martani daga wasu ’yan siyasa. Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, ya taɓa gargadin cewa kallon matsalar tsaro a matsayin ta addini kaɗai na iya ɓata sunan ƙasar a idon duniya, yana mai cewa rikicin ya shafi ta’addanci, fadan makiyaya da manoma da kuma ayyukan ’yan bindiga.

Hukumomin Najeriya dai sun sha nanata cewa matsalar tsaron ƙasar ba ta ta’allaka ne ga tsangwamar addini daga gwamnati ba, sai dai ta samo asali ne daga ta’addanci, fashi da makami da rikice-rikicen ƙabilanci.

Miƙa wannan rahoto na zuwa ne a matsayin mataki mafi girma tun bayan sake ayyana Najeriya a jerin CPC, lamarin da ka iya sauya alkiblar hulɗar diflomasiyya tsakanin Washington da Abuja, musamman kan batun tsaro da kuma bin diddigin ’yancin addini.

Comments (0)
Add Comment