An ƙaddamar da gwamnatin bayan fage wadda za ta rika nazarin manufofin gwamnati da farfaɗo da rayuwar al’umma

Farfesa Pat Utomi, mashahurin masanin tattalin arziƙi kuma ɗan gwagwarmaya, ya ƙaddamar da gwamnatin bayan fage mai suna Big Tent Coalition Shadow Government, wadda za ta rika nazarin manufofin gwamnati tare da ba da shawarwari kan hanyoyin farfaɗo da rayuwar al’umma.

A cikin taron bidiyo da aka gudanar a daren Litinin, Farfesan ya ce wannan gwamnati za ta mayar da hankali kan fannonin ilimi, da lafiya, da tsaro da gyaran tsarin mulki, duk da cewar Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya soki tsarin yana mai cewa ba shi da tushe a dokar Najeriya.

Utomi ya bayyana matsalar sauya jam’iyya da rikicin Benue da Plateau a matsayin alamu na rashin kwarewar gwamnati, yana mai cewa idan ‘yan adawa suka yi shiru, za su taimaka wajen raunana zaɓin talakawa.

A cewarsa, gwamnatin bayan fagen za ta riƙa zama mako-mako domin samar da tsare-tsare da za su tallafa wa rayuwar al’umma ta hanyar kishin ƙasa da bin sahihin shugabanci.

Comments (0)
Add Comment