An binne hakimin da ‘yan bindiga suka kashe tare da ɗansa a Sakkwato
An binne Hakimin ƙauyen Kulodo da kuma babban ɗansa tare da wasu mutum huɗu da ‘yan bindiga suka kashe bayan hare-haren da suka kai ƙauyukan Kulodo da Kwamtsi da ke Ƙaramar Hukumar Bodinga a Jihar Sakkwato.
Aminiya ta ruwaito yadda maharan suka kashe mutum biyar a ƙauyen Kulodo, yayin da wani mutum guda ya rasa ransa a ƙauyen Kwamtsi.
Haka kuma, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutum huɗu, yayin da wasu biyu suka jikkata.
Mazauna yankin sun ce harin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis.
Sai dai ba a samu damar kwashe gawarwakin waɗanda aka kashe ba sai da yammacin ranar Juma’a, saboda fargabar ‘yan bindiga na iya sake kai wani sabon harin.
Wani jami’in ƙungiyar agaji ta Red Cross a Najeriya, Ahmad Suleiman, ya ce ma’aikatan ƙungiyar sun haɗa kai da jami’an tsaro da mazauna yankin wajen kwashe gawarwakin tare da yin jana’izarsu bisa koyarwar addinin Musulunci.
Wani mazaunin yankin ya ce kimanin ‘yan bindiga 150 ne suka mamaye ƙauyukan a kan babura, inda kowane babur ke ɗauke da mutum biyu ko uku ɗauke da makamai.
Ya ce ‘yan bindigar sun kewaye ƙauyukan tare da harbi ba ƙaƙkautawa, sannan suka shuga gidaje da shaguna, inda suka sace dabbobi sama da 200 da sauran kayayyaki.
Ya ƙara da cewa yawancin waɗanda aka kashe an harbe su ne a cikin gidajensu yayin da suke ƙoƙarin ɓuya.
Haka kuma, ya ce an kashe Hakimin ƙauyen Kulodo da babban ɗansa a ƙofar gidansu yayin da suke ƙoƙarin tserewa.
Wani dattijo a yankin ya ce maharan sun kuma kwashe kuɗi, wayoyi da sauran kayayyaki a gidajen da suka shiga.
Ya ce wani mazaunin yankin mai suna Alhaji Shehu ya yi asarar sama da Naira miliyan ɗaya da kuma shanu sama da 40 a yayin harin.
Mazauna yankin sun yaba wa jami’an gwamnati, hukumomin tsaro, sojoji, jami’an DSS da kuma ma’aikatan agaji bisa rawar da suka taka wajen kwashe gawarwakin da tabbatar da cewa an yi wa mamatan jana’iza.
Kafin yin jana’izar mamatan a Kulodo, an riga an yi jana’izar wani daga cikin waɗanda aka kashe a yayin harin a fadar Hakimin Gundumar Bodinga.