Mazauna da shugabannin al’umma a ƙaramar hukumar Bassa ta Jihar Filato sun yi jana’izar mutum bakwai da aka kashe a wani hari da ’yan bindiga suka kai a yankin.
An gudanar da jana’izar ne a wata makarantar firamare da ke Miango, mako guda kacal bayan binne wasu mutum tara da aka kashe a wani hari a Dorowa Babuje da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi. anyi jana’izar tare da zanga-zanga ta nuna fushin jama’a kan ci gaba da tashin hankali a yankin.
Masu makoki sun riƙe alluna dauke da rubuce-rubuce kamar haka “Rayukan Irigwe na da muhimmanci,” “A dakatar da kisan Kiristoci,” “A kawo ƙarshen kisan Kiristoci a Najeriya,” “Ku saurari kukan zawarawanmu,” da kuma “Adalci ga waɗanda aka kashe.”
Shugaban ƙungiyar matasan Irigwe ta ƙasa, Ezekiel Bini, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai cewa sun gaji da binne mutanensu, kuma suna buƙatar adalci da kariya ga al’ummarsu.
Ya ce sun yi zaton hare-haren za su tsaya bayan shafe shekaru kusan ashirin ana fama da matsalar, amma har yanzu ba a samu sauƙi ba. Ya kuma bayyana cewa suna ganin ana watsi da koke-kokensu, musamman idan sun yi magana kan zargin kisan Kiristoci.
Bini ya kuma soki kama wasu ’yan ƙabilar Irigwe kan wasu al’amura da ba su da alaƙa da hare-haren, yana mai cewa ba za su ɗauki alhakin abin da ba su sani ba.
Sarkin Irigwe, Mai Martaba Ronku Aku, ya bayyana ranar a matsayin “rana mai duhu ga al’ummarmu.” Ya ce babbar matsalar yankin ita ce kiwon dabbobi a fili, yana mai jaddada cewa dole ne a dakatar da shi domin a samu zaman lafiya.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta shiga tsakani, yana mai cewa ba za a iya zama shugaba ba idan babu jama’a.
Shugaban ƙaramar hukumar Bassa, Joshua Riti, ya ba mazauna tabbacin cewa suna aiki tare da jami’an tsaro domin cafke masu kai harin.
Daga cikin waɗanda aka binne har da Abbas Musa, wanda ya kammala karatu a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Enugu, kuma jami’in lafiya ne a ƙaramar hukumar Bassa. An harbe shi har lahira a gidansa ranar Litinin, 23 ga Fabrairu, 2026.
Sauran waɗanda aka kashe sun haɗa da mutum biyar ’yan gida daya – Nancy Monday, Nuhu Isaiah, Henry Dah, Zongo Sunday da Tarma Monday – waɗanda rahotanni suka ce maharan sun bi su har cikin dakunansu suka kashe su a ranar 26 ga Fabrairu, 2026.
Hare-haren sun ƙara tayar da hankula a yankin, inda mazauna ke kira da a ƙara tsaurara matakan tsaro domin kauce wa sake asarar rayuka.