Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta dage shari’ar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zuwa ranar 23 ga Afrilu, 2026, bayan da bai gurfana a gaban kotun ba a zaman da aka yi ranar Laraba.
A zaman da aka koma domin gurfanar da shi, lauyan masu gabatar da kara, Oluwole Aladedoye, ya shaida wa kotun cewa duk da cewa an shirya zaman ne domin a gurfanar da wanda ake tuhuma, ba a samu damar kawo shi ba, domin a halin yanzu yana hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta, wato ICPC. Ya roki kotun da ta dage shari’ar zuwa 10 ga Maris domin bai wa hukumar damar gabatar da shi, yana mai cewa Hukumar DSS ba ta da iko a kan ICPC.
Sai dai lauyan wanda ake kara, Oluwole Iyamu, ya ce ba sa da adawa da dage zaman, masu gabatar da karar sun tabbatar a gaban kotu cewa laifukan da ake tuhumar sa da su na da damar beli. Daga nan ne bangaren kariya ya nemi kotu ta fara sauraron bukatar beli kafin a ci gaba da shari’ar.
Amma masu gabatar da kara sun yi adawa da hakan, suna rokon kotun da ta dakatar da batun beli na tsawon makonni biyu. Lauyan kariya ya ce tsare wanda yake karewa na karin makonni biyu zai zama tauye masa hakki, yana mai jaddada cewa har yanzu ba a gurfanar da shi a gaban kotu ba. Ya kuma ce ba bangaren kariya ne ya tsare shi ba, don haka ba su da ikon gabatar da shi a kotu, yana mai cewa da a ce Hukumar DSS ce ke tsare da shi, da lamarin zai kasance daban, tare da rokon kotun ta yi amfani da ikon da kundin doka ya ba ta domin a gabatar da shi.
A hukuncin da ta yanke kan muhawarar, Mai shari’a Joyce Abdumalik ta ce tun da har yanzu ba a gurfanar da wanda ake kara ba, batun beli bai taso ba. Ta danganta hukuncin da sashe na 156 na Dokar Gudanar da Shari’o’in Laifuka ta shekarar 2015, inda ta bayyana bukatar belin a matsayin wacce ta zo kafin lokaci. Daga nan kotun ta dage shari’ar zuwa 23 ga Afrilu, 2026 domin gurfanar da shi.
Rahotanni sun ce a ranar 16 ga Fabrairu, 2026, Hukumar DSS ta shigar da tuhume-tuhume uku a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, tana zargin El-Rufai da kutse cikin sadarwar wayar Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Nuhu Ribadu. Ana zargin cewa tsohon gwamnan ya amince a wata hira da ya yi a gidan talabijin na Arise TV cewa shi da wasu sun shiga cikin lamarin. Ana cewa laifukan na karkashin Dokar Yaki da Laifukan Intanet ta 2024 da kuma Dokar Sadarwa ta Najeriya ta 2003 ne.
A gefe guda kuma, tsohon gwamnan ta hannun lauyoyinsa ya shigar da wata bukata a gaban kotu yana neman a soke tuhume-tuhumen da ake masa, yana mai cewa sun saba wa kundin tsarin mulki kuma cin zarafin tsarin shari’a ne. Haka kuma ya nemi kotu ta umarci DSS ta biya shi diyyar Naira biliyan biyu, bisa zargin cewa ana amfani da tsarin shari’a ne wajen takura masa da bata masa suna a bainar jama’a.
.